Qatar ta sallami kocin 'yan kwallonta Bruno Metsu

metsu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Metsu ne ya jagoranci Senegal a shekara ta 2006

Qatar ta kori mai horadda 'yan kwallonta Bruno Metsu saboda rashin taka rawar gani a gasar cin kofin kasashen Asiya.

Kasar wacce zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022,ana saran zata dauki hayar koci wanda yayi suna a duniya don maye gurbin Metsu.

Metsu wanda ya maye gurbin Jorge Fossati a shekara ta 2008, yayi tangal tangal tun zuwanshi Qatar, saboda ya kasa tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a bara.

Haka kuma bai wuce zagayen gabda na kusada karshe ba a gasar cin kofin kasashen Larabawa.

A mako mai zuwa ne ake saran za a sanarda sunan wanda zai maye gurbin dan Faransa Metsu.