Hayatou ba zai kalubalanci Blatter ba

Hakkin mallakar hoto none

Shugaban hukumar kwallon kafa na Afrika, Issa Hayatou, ya ce ba zai nemi kujerar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya ba, wato FIFA.

Hayatou dai ya kalubalanci shugaban hukumar Sepp Blatter a takarar neman kujerar a shekarar 2002, amma sai ya sha kasa.

A yanzu haka dai Blatter zai sake tsaya takara a zaben da hukumar za ta gudanar a watan Yuni, amma Issa Hayatou ya ce ba zai nemi tsayawa ba.

"Muna aiki kut da kut tare da Blatter, domin ciyar da FIFA gaba." In ji Hayatou.