Torres ya kai fam miliyan 70- Benitez

Image caption Rafeal Benitez

Tsohon kocin Liverpool Rafael Benitez ya bayyana cewa a kiyasta kudin saida Fernado Torres ne a bara a kan miliyan.

Kocin harwa yau ya bayana aniyarsa na sake horon kungiyar a nan gaba.

Torres dai ya koma Chelsea ne a ranar litinin din da ta gabata a kan fam miliyan hamsin, inda ya fi kowani dan wasa tsada a Burtaniya.

Kungiyar Inter Milan dai ta sallami tsohon kocin Liverpool Benitez bayan ya yi aiki tare da ita na tsawon watanni shida.