CHAN:Nijer ta samu nasara, an doke Ghana

chan Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Najeriya da Kamaru ba su sami cancantar shiga gasar ba

Afrika ta Kudu ta fara da kafar dama a takarar gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika na 'yan wasan dake taka leda a cikin gida wato CHAN bayan ta doke Ghana daci biyu da daya.

Ghana ce ta fara zira kwallo ta kafar Daniel Coomson, sannan bayan a dawo hutun rabin sai Collins Zimba da Leonard Shabangu suka taimakawa Afrika ta Kudu ta samu nasara.

A daya wasan rukunin B, Nijer ta doke Zimbabwe daci daya me ban haushi.

Adamou Abdoulkader ne yaci wa Nijer kwallo a minti na saba'in.

A halin yanzu Nijer zata hadu da Afrika ta Kudu a ranar Laraba a yayinda Ghana zata fafata da Zimbabwe.

A rukunin farko, Aljeriya ta doke Uganda daci biyu da nema sai mai saukin baki Sudan wacce ta samu galaba akan Gabon daci daya me ban haushi.