Torres ya gamu da rashin sa'a a Chelsea

torres
Image caption Chelsea ta sayi Torres daga Liverpool akan pan miliyan 50

Wasan farkon da Fernando Torres ya bugawa Chelsea ya karke ne a rashin nasara inda tsohuwar kungiyarshi Liverpool ta doke su daci daya me ban haushi a filin Stamford Bridge.

Torres dai su daya tal ya kai harin cin kwallo inda Jamie Carragher ya hana kwallon wucewa, kafin a cire Torres daga wasan a minti na 66.

Maxi Rodriguez ya kai hari inda kwallon ta buga karfen raga kafin Raul Meireles ya ciwa Liverpool a minti na 69.

Shima Florent Malouda ya yi kokari matuka inda ya kai harin zira kwallo amma sai gola ya kabe abinda ya baiwa bakin nasara akan 'yan gida.

Kocin Liverpool Kenny Dalglish shine ya fi nuna kwazo wajen dabara akan na Chelsea Carlo Ancelotti, abinda yanzu ke nuna cewar Manchester United ta dara Chelsea da maki 10 kuma da kamar wuya Chelsea ta kare kofinta na gasar premier din.

Ita kuwa Liverpool a yanzu Chelsea ta fita da maki shida ne kacal.