Evra yaki yafewa Faransa kudin gasar cin kofin duniya

evra
Image caption Patrice Evra

Tsohon kaptin din tawagar 'yan kwallon Faransa Patrice Evra na daga cikin 'yan wasan kasar da suka ki yafe kudin garabasarsu na gasar cin kofin duniya.

Shugaban hukumar kwallon Faransa Fernand Duchaussoy a ranar Lahadi ya bayyana cewar sauran 'yan wasan sune William Gallas da Nicolas Anelka da Andre-Pierre Gignac da kuma Marc Planus duk sunki maido da takardar cewar sun yafe kudin garbasar.

Duchaussoy yace "akwai matsala, saboda Patrice Evra yaki maidoda takardar yafe kudin".

Ya kara da cewar sauran 'yan kwallon sun amince da yafe kudin da suka kai kusan dala dubu dari da hamsin kowanne dan kwallo.

Duchaussoy yace za a rarraba kudin ga kulob din da kowanne dan kwallo ya fara buga wa da kuma kwallon amacuwa.

A lokacin gasar cin kofin duniya an gudanar da bore a cikin tawagar 'yan kwallon Faransa abinda yasa aka hukunta Anelka da Evra da sauransu.