West Bromwich Albion ta kori Roberto di Matteo .

matteo
Image caption Da maki biyu West Brom ta wuce rukunin kulob uku na karshe

Kungiyar West Bromwich Albion ta kori mai horadda 'yan kwallonta Roberto di Matteo a ranar Lahadi.

Matakin ya biyo bayan kashin da kungiyar ta sha a wajen Manchester City daci uku da nema a ranar Asabar.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce "A yau mun sallami Roberto daga mukaminshi kuma ya tafi ba tare da wata wata ba".

Ta kara da cewar"wannan matakin da darektocin kulob din suka dauka bisa dalilan doke kulob din da aka yi a karawa 13 cikin wasanni 18".

Michael Appleton ne zai maye gurbinshi kafin a nada wanda zai rike mukamin da dun dun dun.

Di Matteo tsohon dan kwallon Italiya wanda ya taka leda a Lazio da Chelsea, an nadashi kocin West Brom ne a watan Yunin 2009.