Qatar 2022:Za ayi gasar lokacin matsanancin zafi-Blatter

qatar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blatter ya mikawa Sarkin Qatar kofin gasar kwallon duniya

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya bada tabbacin cewar za a gudanar da gasar cin kofin duniya na shekara ta 2022 a Qatar lokacin zafi a maimakon lokacin sanyi da ake yita kiraye kiraye akai.

A baya Blatter ya bayyana cewar za ayi gasar a watan Junairu saboda yanayin zafin kasar Qatar.

Bisa al'ada a watan Yuni da Yuli ne ake gasar amma saboda yanayin Qatar inda a wannan lokacin ma'aunin yanayi kan kai arba'in bisa mizanin selshious (40C), ake tunanin ya kamata a canza.

Blatter ya shaidawa BBC:"Ina tunanin a lokacin da za a gudanar da zaben a yanayin zafi ne, mun kamalla batun saboda za ayi wasanni 64 a Qatar".

A watan Junairu, Blatter ya ce Qatar ta samu damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a yanayi na zafi,amma za a iya sauya lokacin don kariyar 'yan kwallon saboda matsanancin zafi".

Tun da farko dai tsohon kocin Jamus Franz Beckenbauer da shugaban Uefa Michel Platini sun nemi a sauya lokacin gudanar da gasar ya koma lokacin sanyi.