Guardiola ya sabunta yarjejeniya da Barca

Image caption Guardiola ya lashe kofuna takwas a Barca kawo yanzu

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya amince ya sabunta yarjejeniyarshi da kungiyar har zuwa karshen kakar badi.

Kwantiragin Guardiola dai za ta kare ne a karshen kakar bana, amma kulob din ya nemi shi ya ci gaba da zama saboda nasarorin da ya samu.

"Za a sanya hannu kan yarjejeniyar ne a 'yan kwanaki masu zuwa," a cewar kulob din.

Kocin mai shekaru 40, ya lashe kofuna takwas kawo yanzu, ciki har da La Liga biyu da gasar zakarun Turai a 2009, tun bayan zuwansa a shekara ta 2008.

A yanzu haka Barca na saman teburin la Liga da maki bakwai, kuma sun zamo kulob na farko da ya lashe wasanni 16 a jere a gasar La Liga.