Spartak Moscow na zawarcin Roman Pavlyuchenko daga Spurs.

Roman Pavlyuchenko
Image caption Roman Pavlyuchenko

Kungiyar Spartak Moscow ta Rasha na zawarcin dan kwallon Tottenham Roman Pavlyuchenko.

A baya Spartak ta nemi sayen Pavlyuchenko amma Spurs tayi burus bata bada amsa ba.

Darektan wasanni Dmitri Popov ya bayyana cewar "Roman Pavlyuchenko gogaggen dan kwallo ne wanda ya kware wajen zira kwallo, muna son ya buga mana kwallo".

Kocin Tottenham Harry Redknapp a baya ya ce ba zai siyar da Pavlyuchenko saboda ya bar Robbie Keane ya hade da West Ham a watan daya wuce.

Pavlyuchenko ya gano bakin zaren a Tottenham a kakar wasa ta bana inda kawo yanzu yaci kwallaye tara, sai dai yana fuskantar kalubale daga wajen Rafael van der Vaart da Peter Crouch da kuma Jermain Defoe.