Nasri na fatan Wilshere zai haskaka a Ingila

Image caption Wilshere ne matashi na goma da ya fara taka wa Ingila leda a shekara 18

Dan wasan tsakiya na Arsenal Samir Nasri na da imanin cewa Jack Wilshere zai haskaka a daidai lokacin da yake shirin fara takawa Ingila leda.

Ana saran Wilshere, dan shekaru 19, zai buga wasa cikakke na farko a Ingila a wasan sada zumuntar da kasar za ta yi da Denmark.

Kuma Nasri ya ce abokin wasan nasa a Arsenal ba zai rude ba, ya gayawa BBC Radio 5: "Ina son yadda Jack yake taka leda, ba shi da tsoro ko kadan.

"Halayyarsa tana burge ni, kuma yana tunamin lokacin da na ke matashi. Yana da makoma mai kyau."

Wilshere ya zamo matashi na goma da ya fara taka wa Ingila leda a shekara 18, kuma kwanaki 222 bayan da ya maye gurbin Gerrard a wasan Ingila da Hungary a filin wasa na Wembley.