Ingila ta doke Denmark a wasan sada zumunta

Image caption Fabio Capello ya yi farin ciki kan yadda 'yan wasan suka taka rawar gani

Ingila ta fara shekara ta 2011 da kafar dama bayan da ta doke Denmark da ci 2-1 a wasan sada zumunta a birnin Copenhagen.

Daniel Agger ne ya fara zira wa Denmark kwallon farko bayan mintina bakwai da fara wasan. Sai dai nan take Darren Bent ya rama wa Ingila.

Christian Eriksen ya kai mummunan hari yayin da mai tsaron gida Joe Hart ya hana Dennis Rommedahl.

Sai dai Ashley Young da ya shigo wasan bayan an dawo hutun rabin lokaci ya zira wa Ingila kwallo ta biyu.

Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya taka rawar gani a wasan, kuma koci Fabio Capello ya nuna farin ciki kan yadda 'yan wasan suka taka rawar gani.

Sakamakon wasannin sada zumuntar da aka buga

Argentina 2-1 Portugal Italiya 1-1 Jamus France 1-0 Brazil Spain 1-0 Colombia Holland 3-1 Austria Iran 1-0 Rasha Poland 1-0 Norway South Africa 2-0 Kenya