Branislav Ivanovic ya sabunta yarjejeniyarshi a Chelsea

ivanovic Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Branislav Ivanovic

Dan kwallon bayan Chelsea Branislav Ivanovic ya sabunta yarjejeniyarshi da kungiyar zuwa shekara ta 2016.

A watan Junairun shekara ta 2008 ne dan kwallon Serbia mai shekaru ashirin da shida ya koma Stamford Bridge.

Ya bugawa Chelsea kwallo a karawa 99 kuma a kakar wasannin data wuce ya samu kyauta ta musamman saboda taka rawar gani.

Ivanovic yace "wannan labari ne me kyau gare ni, ina son in taimakawa Chelsea ta kara samun kyautuka da dama".

A shekaru ukun da Ivanovic ya shafe a Chelsea, ya lashe kofinan gasar FA biyu da kuma gasar premiership sau guda a yayinda ya zira kwallaye bakwai.