Sulley Muntari zai gani bakin zaren a Sunderland

muntari
Image caption Sulley Muntari

Dan kwallon bayan Sunderland Titus Bramble yace sabon dan wasansu Sulley Muntari zai kara fahimtar kulob din nana bada jimawa ba.

Muntari mai shekaru ashirin da shida ya koma Sunderland ne a matsayin aro bayan ya buga wasanni goma sha a kakar wasa ta bana a Inter Milan.

Bramble ya shaidawa BBC cewar"Sulley na daga cikin zaratan 'yan kwallonmu".

Dan kwallon Ghana wanda ya taba bugawa Portsmouth kafin ya koma Inter Milan, ya zira kwallaye 17 a wasanni 56 daya bugawa kasarshi.

Bramble ya kuma jinjinawa dan kwallon Benin Stephane Sessegnon wanda aka siyo daga Paris Saint Germain akan pan miliyan shida.