Zan bar Marseille a karshen kakar wasan bana-Taiwo

taiwo
Image caption Taye Taiwo

Dan kwallon Najeriya Taye Taiwo ya tabbatar da cewa zai fice daga kungiyarshi ta yanzu Marseille a karshen kakar wasa ta bana.

Yarjejeniyar Taiwo da Marseille zata karke ne a karshe kakar wasa ta bana.

A baya rahotanni sun nuna cewar wasu kulob na gasar premier irinsu Tottenham da Newcastle United sun nuna shawa'ar sayen dan kwallon.

A hirar da yayi da wata jarida a Najeriya, Taiwo ya ce sun fara tattaunawa akan batun canza shekar zuwa Ingila.

Dan kwallon Najeriya mai shekaru ashirin da biyar ya ce"Na yanke shawarar kin sabunta yarjejeniya ta a Marseile".