Babu gaba tsakani na da Cristiano - Messi

Ronaldo_Messi
Image caption Duka 'yan wasan biyu sun zira kwallaye 24-24 a gasar La Liga ta bana

Gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi ya ce babu wata gaba tsakaninsa da shahararren dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo.

Duka 'yan wasan biyu sun zira kwallaye 24-24 a gasar La Liga ta bana, kuma a ranar Laraba sun hadu gaba-da-gaba, a wasan sada zumuntar da Argentina da buga Portugal.

Messi ya buga fanareti a mintin karshe wanda ya baiwa Argentina nasara da ci 2-1 a kan Portugal.

Messi ya ce: "Wannan ba wasa bane tsakanin Barcelona da Real Madrid ko tsakanin Ronaldo da Messi," kamar yadda ya shaida wa shafin intanet na Uefa.com

"Ba muna yin wasa ba ne domin nuna wanda ya fi wani, muna yi ne domin taimakawa kungiyoyinmu.

Ya kara da cewa "An sani na buga wasan baki daya, kuma an samu fanareti na buga kamar yadda na saba bugawa a kodayaushe".

Shi ma dai Ronaldo shi ya zira kwallo dayan da Portugal ta zira a wasan.