AC Milan ta kara tazara akan teburin gasar Italiya

zltan
Image caption Zlatan Ibrahimovic da Clerence Seedorf

AC Milan ta samu kwarin gwiwa a shirye shiryenta na fuskantar Tottenham a gasar zakarun Turai, bayan da Milan din ta lallasa Parma daci hudu da nema a gasar serie A.

Kenan AC Milan ta buga wasannin goma a jere ba a doketa ba,a yayinda sabon dan kwallonta Antonio Cassano ya zira kwallonshi na farko tun zuwan San siro daga Sampdoria a watan daya gabata.

Tsohon dan kwallon Manchester City Robinho shima ya zira kwallaye biyu a yayinda Clarence Seedorf yaci kwallo daya.

Sakamakon karawar karshen mako a Italiya:

*Palermo 2 - 4 Fiorentina *Cagliari 4 - 1 Chievo *Bari 0 - 0 Genoa *Brescia 0 - 2 Lazio *Catania 3 - 2 Lecce *Cesena 0 - 3 Udinese *Sampdoria 3 - 1 Bologna *Milan 4 - 0 Parma *Roma 0 - 2 Napoli