Babu matsala don mun tashi canjaras-Guardiola

guradiola
Image caption Pep Guardiola

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya ce babu damuwa don 'yan wasanshi sun kasa doke Sporting Gijon a wasansu na gasar La Liga a ranar Asabar.

Barcelona ta sha mamaki ne tun a minti goma sha shida da fara wasan inda David Barral ta zira kwallon farko sannan David Villa ya farke ana sauran minti 10 a tashi wasan.

Canjaras din da Barca ta tashi ya janyo Real Madrid zata rage tazarar dake tsakaninta sa Barca, inda har Real din ta samu galaba akan Espanyol.

Amma Guardiola yace"mun yi kokarin samun nasara amma abin bai yiwuwa ba".

Kocin kuma yaki yarda da batun cewar wasannin sada zumuncin da 'yan kwallo suka bugawa kasashensu na gado a tsakiyar mako shine abinda ya janyowa Barca cikas.

"Babu laifin tawagar kasashe,anan Barca muna buga wasa kusan a kowanne kwanaki uku", in ji Guardiola.