Mun taka rawa mafi muni - David Moyes

David Moyes
Image caption David Moyes ya shafe shekaru tara a Everton

Kocin Everton David Moyes ya ce kashin da kungiyar ta sha a hannun Bolton da ci 2-0 shi ne mafi muni da ya taba fuskanta a shekaru taran da ya shafe a kungiyar.

Kwallaye biyu ta hannun Gary Cahill da Daniel Sturridge ya jefa Everton cikin tsaka mai wuya, inda suke gab da fada wa jerin kungiyoyin da ke kasan tebur.

Ya ce "Ba mu yi kokari ba, 'yan wasan da suka saba taka leda sosai, amma yau sun taka mummunar rawa".

Moyes ya kuma yi Allah wadai da matakin da alkalin wasa ya dauka na soke kwallon da Cahill ya zira a minti goma da fara wasan.