CHAN:Nijer ta tsallake bayan ta casa Ghana

nijer
Image caption Jamhuriyar Nijer ta kafa tarihi

Jamhuriyar Nijer ta kafa tarihi a gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika na 'yan wasan dake taka leda a cikin gida wato CHAN inda ta tsallake zuwa zagayen gabda na kusada karshe a karon farko bayan ta doke Ghana daci daya me ban haushi.

Menas din sun fidda Ghana wacce ta samu kyautar azurfa a gasar da akayi a shekara ta 2009.

Nijer bata taba shiga gasar kwallo a mataki na nahiyar Afrika ba sai a wannan karon kuma Gambo Tukur ya zira kwallon ana gabda tashi wasan.

Afrika ta kudu ce ta zama ta farko a rukunin bayan ta doke Zimbabwe daci biyu da daya.

Nijer ta kasance ta biyu da maki shida, a yayinda ita kuma Afrika ta Kudun ta samu maki tara.

Nijer zata hadu da Sudan a ranar Juma'a sai kuma Afrika ta Kudu ta kece raini da Aljeriya.