Golf:An ci tarar Tiger Woods saboda tofar da miyau

woods
Image caption Tiger Woods

An ci tarar shahararren dan wasan golf, Tiger Woods saboda tofar da yau a wajen gasa lokacin Dubai Desert Classic.

Ya tsidda yau dinne 'yan mintuna kusada ramin da kwallon golf ke shiga bayanda ya kuskure a ranar Lahadi.

An kama Woods ta laifin saba ka'idar gasar golf na Turai, a don haka za aci tararshi kudaden da ba a san yawansu ba.

Abar daukar hoto ne ya gano Woods yana tofar da yau, inda aka ganshi yana gungunai.

Bai taka rawar gani ba a gasar ta Dubai kuma watanni goma sha hudu kenan rabon daya lashe wata gasa.

A baya ya samu kyautuka 14 abinda yasa ake ganin a matsayin daya daga cikin wadanda suka kafa tarihi a fagen golf.