Park Ji-Sung zai yi jinyar mako hudu

Park Ji-Sung
Image caption Dan wasan mai shekaru 29 ya dawo horo ne a makon da ya gabata

Dan wasan Manchester United Park Ji-Sung zai yi jinyar makwanni hudu sakamakon raunin da ya samu.

Dan wasan mai shekaru 29 ya dawo horo ne a makon da ya gabata bayan ya shafe wata guda yana jinya sakamakon raunin da ya samu a gasar cin kofin kasashen Asia a Qatar.

"Mun samu koma baya sakamakon raunin da Park ya samu," a cewar Sir Alex Ferguson kocin Manchester United.

Ya kara da cewa: "Zai shafe makonni hudu ba ya taka leda."

Dan wasan ba zai buga wasan da United za ta yi da Crawley a gasar FA, da kuma Marseille a gasar zakarun Turai da wasannin Premier da Wigan da Chelsea da kuma Liverpool.