CHAN:Nijer bata tsohon kowacce kasa a duniya

Idrissa Laouali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idrissa Laouali na tawagar Mena

Mataimakin shugaban hukumar dake kula da kwallon Nijer ya ce kasar zata doke mai masaukin baki wato Sudan a wasan zagayen gabda na kusada karshe na gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika na 'yan kwallon cikin gida wato CHAN.

Kanar Ibrahim Yacoub ya ce Nijer zata iya tsallakewa zawa wasan karshe.

Wannan ne karon farko da Nijer ta kai irin wannan matakin a fagen kwallon manya a nahiyar Afrika.

Ya ce "Tawagar Mena bata jin tsoron kowacce kasa a duniya, kuma muna da karfin taka rawar gani".

Nijer a baya bata taba shiga takara a gasar cin kofin kwallon Afrika ba.

Mena ta bada mamaki inda ta doke Ghana daci daya me ban haushi a wasan zagayen farko, nasarar data bata damar samun gurbi a zagayen gabda na kusada karshe.

Kanar Ibrahim Yacoub ya ce Nijer zata maida hankali wajen samun gurbi a gasar cin kofin duniya dana kofin Afrika a nan gaba.