UEFA ta fara bincike akan rashin da'ar Gattuso

gatuso Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gattuso ya makure Joe Jordan

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Turai-Uefa ta fara gudanar da bincike akan batun rashin da'a akan dan kwallon AC Milan Gennaro Gattuso bayan ya yiwa mataimakin kocin Tottenham Joe Jordan karon kai.

Lamarin ya auku ne bayan da aka tashi wasan inda Spurs ta doke Milan daci daya me ban haushi a bugun farko na zagaye na biyu na gasar zakarun Turai a filin San Siro.

Dan kwallon Italiyan kuma tsohon dan wasan Rangers din Gattuso ya nemi afuwa akan lamarin.

Gattuso ya ce"Raina ya badi,kuma bani da hujjar yin abinda na yi,na amsa laifi na".

Gattuso mai shekaru talatin da uku tun kafin a tashi wasan ya samu rashin jituwa da Jordan mai shekaru hamsin da tara a lokacin da dan wasan AC Milan Mathieu Flamini ya tokari dan Tottenham Vedran Corluka.

Sakamakon tokarin dai, saida aka fidda Corluka daga cikin fili sannan daga bisani ya dawo da sanduna ya zauna a benci tare da sauran 'yan kwallon Spurs a yayinda aka daure mashi idon sawu da kankara.