Uefa: Za a biya akalla pan 176 don kallon wasan karshe

uefa
Image caption Tambarin gasar zakarun Turai

'Yan kallo zasu biya pan akalla 176 na tikitin kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai da za a buga a filin Wembley a ranar 28 ga watan Mayu.

Sai dai magoya bayan kungiyoyin da zasu fafata a wasan karshen zasu sayi tikitin akan pan tamanin.

Darektan kula da gasa a Uefa Giorgio Marchetti ya ce an kayyade farashinne bisa la'akari da yanayi irin na gasar cin kofin duniya.

Yace "bama tunanin aka lafta kudin kallon wasan karshe na gasar zakarun Turai".

Marchetti ya ce"mun tsara yadda lamarin yake, tare da lura da farashin tikitin gasar kwallon kasashen Turai na gasar kwallon duniya".

Uefa ta sanarda cewar tikiti dubu goma sha daya ne za a siyarwa jama'a.

Farashin tikitin banda kudin ma'aikatan lura da aikin shine pan 150 zuwa 225 zuwa 300 a yayinda guragu zasu biya pan tamanin.

Ya kara da cewar an kebewa magoya bayan kungiyoyin biyu da zasu fafata a wasan karshen tikiti dubu ashirin da biyar.