CHAN:Tunisa ta tsallake, an fidda Kamaru da Nijer

issa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban CAF Issa Hayatou

Tunisia ta tsallake zuwa wasan kusada karshe a gasar cin kofin kasashen Afrika na 'yan kwallon dake taka leda a cikin gida, bayan Tunisia din ta samu galaba akan Congo daci daya me ban haushi.

Angola itama tayi bazatan doke Kamaru a bugun penariti daci bakwai da shida.

Angola a ranar Takata za ta hadu da mai masaukin baki wato Sudan wacce ta casa Nijer a bugun penariti.

Ita kuwa Algeriya a ranar Talata zata fafata ne da Tunisia a daya wasan zagayen kusada karshen.

Congo ce ta lashe gasar ta akayi na farko a Ivory Coast a shekara ta 2009.

Sudan a halin yanzu tanada damar lashe gasar ganin cewar a gidanta ne ake fafatawa .