Kofin FA:Watakila Manchester United ta hadu da Arsenal

chelsea
Image caption Chelsea ce ta lashe gasar kofin FA a 2010

Akwai yiwuwar Manchester United ta kara da babbar abokiya hammayarta Arsenal a zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin FA.

Idan har Arsenal ta doke Leyton Orient a bugu na biyu na zagaye na biyar, bayan da suka tashi daya da daya a bugun farko, tabbas gunners zata kara da 'yan wasan Alex Ferguson a filin Old Trafford.

Manchester City ko Aston Villa zasu dauki bakuncin Everton ko Reading, a yayinda Stoke zata fafata da West Ham ko Burnley, ita kuwa Bolton zata raba tsaki da tsakuwa ne tsakaninta da Birmingham.

Za a buga wasannin zagayen gabda na kusada karshen a ranakun 12 da 13 ga watan Maris.

Yadda aka rarraba kulob kulob:

Stoke v West Ham ko Burnley Man City ko Aston Villa v Everton ko Reading Birmingham v Bolton Manchester United v Leyton Orient ko Arsenal