Mourinho ya kara kafa sabon tarihi a matsayin koci

mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya kafa sabon tarihi na samun nasara a fagen kwallon kafa inda ya shafe shekaru tara ba tare da an doke kulob dinshi a gidanta ba.

Nasarar da Real ta samu akan Lavante daci biyu da nema a gasar La Liga itace ta tabbatar da wannan bajintar ta Mourinho.

Hakan dai na nufin cewar Mourinho ya taka rawar gani a gidan kulob din da yake yiwa jagoranci na tsawon shekaru tara a kungiyoyi hudu daban daban wato FC Porto da Chelsea da Inter Milan da Real Madrid.

Lokaci na karshe da aka doke kungiyar da Mourinho ke yiwa jagoranci a gidanta shine wasan da kungiyar Beira Mar ta doke Fc Porto a ranar ashirin da uku ga watan Fabarairu na shekara ta 2002.

Hakan na nufin cewar Mourinho ya samu nasara a karawa 122 cikin 147.