Dan Ghana Boateng ya komo taka leda a AC Milan

Kevin Prince Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin Prince Boateng

Dan kwallon Ghana Kevin Prince Boateng ya komo taka leda bayan shafe watanni biyu yana jinya.

A wata mai zuwa ne aka saran Boateng zai dawo buga kwallo saboda rauni a idon sawunshi, amma kuma sai ya murmure kafin cikan lokacin da aka diba.

A ranar Lahadi an sakashi bayan an dawo hutun rabin lokaci a karawar da AC Milan ta doke Chievo daci biyu da daya.

Boateng yace"nayi murnar komawa fili kuma yanzu na warke".

Dawowar Boateng zata karawa Ghana kwarin gwiwa a wasan share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika tsakaninta da Congo.

Black Stars nada wasa a ranar ashirin da shida ga watan Maris a birnin Brazzaville a kokarinta na samun gurbi a gasar cin kofin kasashen Afrika a badi a kasashen Gabon da Equitorial Guinea.