Patrice Evra ya sabunta yarjejeniyarshi a Old Trafford

evra
Image caption Patrice Evra

Dan kwallon Manchester United Patrice Evra ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar don cigaba da taka leda a Old Trafford har zuwa karshen kakar wasa ta 2013/14.

Dan wasan Faransa mai shekaru ashirin da tara ya bugawa United wasa a karawa 226 tun bayan da ya bar Monaco a shekara ta 2006 akan pan miliyan biyar.

Kocin United Sir Alex Ferguson Yace: "Patrice na daya daga cikin 'yan kwallon baya mafi gogewa a duniya".

Evra ya taimakawa Manchester ta lashe kofina gasar premier uku dana zakarun Turai daya da kuma na Carling uku.

Ferguson ya kara da cewar tun da Evra ya amince wajen cigaba da takawa United leda, tabbas zai kara samun nasarori da dama.