Claudio Ranieri ya yi murabus a matsayin kocin AS Roma

ranieri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Claudio Ranieri

Tsohon kocin Chelsea Claudio Ranieri ya yi murabus a matsayin mai horadda 'yan wasan AS Roma bayan sun sha kashi a wasanni hudu a jere.

Rashin nasarar da Roma ta tsinci kanta a ciki yasa ta koma ta takwas akan tebur da maki talatin da tara cikin karawar ashirin da biyar.

Ranieri ya jagoranci Chelsea daga shekara ta 2000 zuwa 2004,kafin ya koma took Roma a watan Satumbar 2009.

Dan shekaru hamsin da taran ya taba horadda Juventus da Valencia da kuma Athletico Madrid.

A tsakiyar mako Roma ta sha kashi a gidanta a wasan zakarun Turai a filin Stadio Olimpico inda Shakhtar Donetsk ta samu galaba akanta daci uku da biyu.

Haka zalika, wani kamfanin Amurka DiBenedetto ya bada wa'adin kwanaki talatin don sayen AS Roma wand ke fama da matsalolin kudi.