Mancehster United na Glazers ne dari bisa dari

Man united
Image caption Tambarin Manchester United

Manchester United ta bayyana mahukunta gasar Premier cewar har yanzu iyalan Glazer ne keda kulob din dari bisa dari.

An yita jita jitar cewar iyalan Amurkawan sun sayarda kaso mai tsoka na hannun jarin kulob din don ya biya bashi.

An fara samun shakku ne bayanda Glazers suka yi rajistar wani kamfanin a Delaware, inda basu bayyana masu mallakarshi ba.

Kakakin United ya shaidawa BBC cewar"babu bambanci a masu mallalar kulob din".

Kungiyar magoya bayan kulob din na neman sanin ko iyalan Glazers na kokarin musanya bashin da ake binsu da wani banshi ta hanyar sauya kamfaninsu Red Football LLC daga Nevada zuwa Delaware.

Iyalan Glazer sun sha nanata cewar ba suda niyyar cefanarda United.