West Ham ta doke Burnley da ci 5-1

West Ham Hakkin mallakar hoto PA
Image caption 'Yan wasan West ham na murnar nasarar da suka samu

West Ham za ta kara da Stoke a zagaye na shida na gasar FA, bayan da ta lallasa Burnley da ci 5-1.

Thomas Hitzlsperger ne ya fara zira kwallon farko a wasansa na farko da ya buga a kulob din.

Carlton Cole ne ya zira ta biyu da ta uku, sai dai an yi korafi kan kwallo ta biyu da ya zira, inda ake ganin ya yi satar gida.

Winston Reid da Freddie Sears ne suka zira kwallaye na hudu da biyar, yayin da Jay Rodriguez ya zira kwallo dayan da Burnley ta samu a wasan.