CAF:Bwalya da Nyantakyi sun zama wakilai

bwalya
Image caption Kalusha Bwalya na Zambia

Tsohon gwarzon dan kwallon Afrika Kalusha Bwalya na Zambia ya lashe zaben shiga cikin kwamitin gudanarwar hukumar kwallon kafa ta duniya wato Caf.

Bwalya ya doke wasu mutane hudu a zaben daya gudana a birnin Khartoum na Sudan don kasancewa wakilin yankin kudancin Afrika a hukumar Caf.

Shima shugaban hukumar kwallon Ghana Kwesi Nyantakyi ya samu nasara inda ya samu kuri'y talatin da hudu ya doke Anjorin Moucharafou na jamhuriyar Benin don wakilitar yanki na biyu a yammacin Afrika.

Tsohon kaptin din Tanzania Leodegar Tenga shima ya lashe zabe bayan doke Celestin Musabyimana na Rwanda.

Su kuwa dan Tunisia Tarek Bouchamaoui na yankin arewaci da Omari Constant na jamhuriyar demokradiyar da dan Guinea Almamy Kabele Camara duk sun sake lashe zabukansu ba tare da hammaya ba.