Pep Guardiola ya rattaba hannu a sabuwar kwangila

pep
Image caption Pep Guardiola ya lashe kofina takwas a Barca

Pep Guardiola ya rattaba hannu akan sabuwar kwangilarshi da Barcelona inda zai cigaba da jan ragamar kulob din zuwa karshen kakar wasa ta badi.

Guardiola ya lashe kofin takwas a cikin shekaru fiye da biyu daya shafe a Nou Camp, kuma a yanzu ya wuce Real Madrid da maki biyar a kokarin lashe gasar La Liga a karo na uku a jere.

Kocin dai ya taimakawa Barca ta lashe kofin zakarun Turai dana zakarun kulob na duniya dana Super Cup na Turai, da Copa del Rey da kuma La Liga biyu.

Sai dai ba a bayyana adadin kudaden da za a biyashi ba.

Guardiola ya maye gurbin Frank Rijkaard ne a shekara ta 2008.

Dan shekaru arba'in, tsohon dan kwallon Spain da Barcelona ya ce yafi son ya kulla yarjejeniyar karin shekara guda don cigaba da haskakawar da yake yi a halin yanzu, saboda wannan ne karon da Barca tafi haskaka a tarihinta na shekaru 112.