Kofin Obama:Super Eagles sun isa Amurka

siasia
Image caption Samson Siasia

Tawagar 'yan kwallon Super Eagles na Najeriya sun isa birnin Dallas na Amurka don shiga fafatawa a gasar cin kofin Obama da za a fara ranar Asabar.

'Yan wasa ashirin da kocinsu Samson Siasia zasu buga wasanni biyu ne inda kasashe hudu za suyi takara a gasar da za a buga a filin Cotton Bowl.

Najeriya zata buga wasanta na farko ne tsakaninta da Mexico a ranar Asabar, sannan inda ta samu nasara ta hadu da duk kasar data samu galaba a fafatawa tsakanin Costa Rica da Panama a wasan karshe.

Idan har aka doke Najeriya a wasan farko , to zata buga wasan neman gurbi na uku ne da kasar data sha kaye tsakanin Costa Rica da Panama a ranar Lahadi. Kocin Super Eagles Samson Siasia ya bayyana jin dadinsa akan gasar wacce aka rage yawanta daga kasashe takwas ya koma hudu, inda yace gasar zata kara mashi shiryawa wasan share fage na gasar cin kofin kasashen Afrika tsakaninsu da Ethiopia a ranar 27 ga watan Maris.