Zan bar Munich idan ta siyo Neuer -Kraft

kraft
Image caption Thomas Kraft

Golan Bayern Munich Thomas Kraft ya ce zai bar kulob din idan ta siyo Manuel Neuer daga Schalke 04.

Kraft mai shekaru 22 yana haskakawa matuka a kakar wasa ta bana inda ya taimakawa Bayern a wasanta na zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

A karawar da suka yi da Inter Milan, Kraft ya kabe kwallayen Samuel Etoo dana Cambiasso da Thiago Motta.

Kraft yace"Idan Neuer yazo, zan tafi, saboda babu wata fa'ida in zauna".

Rahotanni sun nuna cewar Manchester United na muradin sayen Neuer don maye gurbinshi da Edwin van der Sar wanda zai yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana.

Kaptin din Bayern Philipp Lahm ya ce Neuer hazikin dan kwallo ne da Bayern ba zata iya bari ba.