Dan Ghana John Mensah ya ce zai fito da kanshi

mensah
Image caption John Mensah

Kaptin din Ghana John Mensah ya ce zai nunawa kocin Sunderland Steve Bruce cewar shi kwararren dan wasa ne da zai iya zama da kafafunsa.

Mensah, tun zuwanshi kulob din ya keta fama da rauni abinda yasa ake tunanin ana gabda cefanar dashi. "Sunderland ta san cewar na taimakawa kasa ta da kuma tsofofin kulob din dana bugawa,kuma suna son in buga musu, tunda sun san ni wani irin dan kwallo ne,"in ji Mensah.

Duk da cewar Mensah ya gasgata cewar baya kan ganiyarshi a kakar wasa ta bana, amma dai ya ce yana saran zai kara fito da kanshi.

A ranar asabar Sunderland za ta buga wasanta da Everton a Goodison Park kuma watakila a saka Mensaha a karawar.