Libya ba za ta samu daukar bakoncin gasar U:20 ba

BBC ta samu labarin cewa Libya ba za ta dauki bakonci gasar cin kofin Afrika ta matasa 'yan kasa da shekara 20 da za a fara a ranar 18 ga watan Maris.

Zanga zangar kin jinin gwamnati da ake yi a kasar ne ya sa Hukumar kwallon Afrika wato CAF ta kwance bakoncin da ta ba kasar.

Wasu majiya sun shaidawa BBC cewa za'a maye gurbin Libya da kasar Afrika ta kudu ko kuma Ghana.

Za'a sanya ranar shirya gasar bayan hukumar CAF ta kammala tattaunawa.