Obafemi Martins ya hana Arsenal daga kofin Carling

martins Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Birmingham City na murnar doke Arsenal

Obefami Martins ya zira kwallo minti daya kafin a tashi wasa inda ya baiwa Birmingham City damar lashe kofinta na farko tun shekarar 1963 a yayinda suka daga kofin Carling a Wembley.

Martins, wanda yazo a matsayin aro daga Rubin Kazan ya yi amfani da daburcewa tsakanin golan Arsenal Wojciech Szczesny da kuma Laurent Koscielny yaci kwallon.

An sako Martins ne inda ya maye gurbin Keith Fahey, kuma wannan kwallon ta kara jefa Arsenal cikin rudu saboda shekaru shida kenan rabon da gunners su lashe wata gasa.

Zigic ne ya ciwa Birmingham kwallon farko sannan Robin van Persie ya farke mata.

Kaptin din Arsenal Cesc Fabregas da Theo Walcott basu buga wasan ba saboda rauni.