Masar ta bukaci CAF ta daga wasanta da Afrika ta Kudu

masar
Image caption Masar ce ta lashe gasar cin kofin Afrika a 2008

Masar ta bukaci hukumar kwallon Afrika Caf ta dage wasanta da Afrika ta Kudu na neman gurbi a gasar cin kofin kasashen Afrika da ya kamata a buga a wata mai zuwa.

Masar ta nemi bukatar yin hakanne saboda tashin hankalin daya auku a kasar a kwanakin baya.

Hukumar Caf ta ce ta samu takardar bukatar Masar din, amma sai nan da kwanaki zata yanke hukunci akai.

Masar nason a daga wasan ranar 26 ga watan Maris a Johannesburg ya koma watan Yuni saboda dakatar da wasan gasar league din kasar da aka sakamakon hargitsin.

Jami'an Masar sun ce yawancin 'yan kwallon Pharaohs a cikin gida suke taka leda, kuma tashin hankali a shafe yadda suke murza leda.

Wasan nada muhimancin gaske ga Masar saboda itace ta biyu a rukunin, a yayinda Afrika ta Kudu ke jan ragama, kuma duk kasar data kamalla a matsayin ta farko itace zata tsallake zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a badi.