Watakila a yiwa Idrissou na Kamaru tiyata a makogwaro

idrissou
Image caption Dan kwallon Kamaru Mohamadou Idrissou

Akwai yiwuwar ayiwa dan kwallon Kamaru Mohamadou Idrissou tiyata a makogwaronshi.

Kungiyar da yake bugawa kwallo a Jamus wato Borrussia Moechengladbach ce ta sanarda hakan a ranar Lahadi.

An fidda Idrissou bayan sa'a guda a wasan da Wolfsburg ta doke su daci biyu da daya, inda daga bisani likitocin kulob din suka bayyana cewar watakila ayi mashi fida a makogwaro.

Dan kwallon mai shekaru talatin ya bugawa Kamaru wasa a karawa 34.

Kawo yanzu dai Idrissou ya zira kwallaye hudu cikin wasanni ashirin da ukun daya bugawa Borrussia Moechengladbach a kakar wasa ta bana, kuma bisa dukkan alamu ba zai buga wasansu na gaba tsakaninsu da Hoffenheim.