Cole zai buga wasanmu na United-Ancelotti

cole Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ashley Cole

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce Ashley Cole zai buga wasansu da Manchester United na ranar Talata duk da tahumar da dan wasan ke fuskanta akan batun harbin wani da bindigar roba.

A farkon wannan watan Chelsea ta ci tarar Cole akan batun harbin wani dalibi.

Dan wasan Ingilan bai san bindigar nada harsashi ba sai ya dauka yana wasa da ita a sansannin horonsu, sai bindigar ta harba kanta ta raunata dalibin.

An zargin Cole da nuna dabi'ar da zata janyowa Chelsea bakin jini, amma dai Ancelotti ya ce hakan ba zai saka dan kwallon cikin damuwar kasa taka leda ba.

Yace"Zai buga wasanmu na ranar Talata, amma dai bamu ji dadin abinda ya faru ba kuma nayi mashi magana".

Ancelotti ya kara da cewar Cole din yayi nadamar abinda ya faru.