Najeriya za ta kai kuka FIFA

NFF Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Hukumar NFF Aminu Maigari

Najeriya na nuna damuwa kan yadda aka dage gasar cin kofin kasashe hudun da aka shirya a Amurka ba tare an sanar da ita ba.

A makon da ya wuce ne dai tawagar Najeriya wacce 'yan wasan cikin gida za su wakilta, su ka riga suka isa birnin Dallas domin fafatawa da Mexico da Panama da kuma Costa Rica.

Amma bayan da suka isa, sai masu shirya gasar suka shaida musu cewa an dage gasar na tsawon mako biyu.

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya Aminu Maigari, ya ce kasar za ta nemi FIFA tasa wadanda suka shirya gasar su biya ta kudaden da ta kashe.

"Zamu hada dukkan yarjejeniyar da muka kulla da su, sannan mu aika wa FIFA," a cewar Maigari wanda shima ya shirya bin tawagar zuwa Amurka.

Shi ma kocin Super Eagles Samson Siasia ya nuna rashin jin dadinsa, domin ya yi niyyar amfani da gasar wajen gwada 'yan wasan cikin gida.

Najeriya za ta kara da Ethiopia a karshen watan Maris a wasan share fagen shiga gasar kasashen Afrika na 2012.