Bamu da matsalar rashin da'a- Ancelotti

Image caption Acelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya musanta rahotanni da ke nuni da cewa kungiyar na fuskantar rashin da'a daga 'yan wasan ta.

Dan wasan bayan kungiyar Ashley Cole ya harbi wani wani dalibi me koyon makamin aiki a kungiyar bisa kuskure a karshen makon daya gabata.

Ancelotti ya ce kungiyar za ta dauki mataki a kan Cole wanda ya raunata dalibin mai shekarun haihuwa 21.

"Bama fuskantar rashin da'a a filin horon mu na Cobham." In ji Ancelotti.

"Duk dan wasan da ya nuna rashin hankali zamu hukunta shi."