Hukumar kwallon Masar ta rage albashin ma'aikata

masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan kasar Masar

Hukumar dake kula da kwallon Masar EFA ta sanarda rage albashin duka ma'aikatanta.

Hakan kuma na iya shafar tawagar 'yan kwallon kasar.

Sanarwar da EFA ta bayar ta ce babu ma'aikacin da zai karbi albashin daya wuce dala dubu biyu da dari biyar sannan karancin albashi zai zama dala dari biyu da hamsin.

An samu tashin hankali na siyasa a Masar, abinda ya tilasta dakatar da harkokin kwallo a kasar da kuma faduwar kudaden haraji.

Sanarwar ta kara da cewar matakin yazo dai dai da sabon tsarin juyin juya halin da kasar ke ciki.

EFA ta ce zata tattauna da kulob kulob na kasar don su amince akan diyyar da za a baiwa 'yan kwallon da aka gayyata zuwa babbar tawagar kasar.