Robin van Persie zai yi jinya ta makwani uku

persie
Image caption Robin van Persie

Arsenal ta gamu da cikas a shirye shiryenta na fuskantar Barcelona a mako mai zuwa a gasar zakarun Turai saboda dan wasanta na gaba Robin van Persie ba zai buga ba.

Dan wasan Holland van Persie wanda yaci kwallo daya a bugun farko tsakanin Arsenal da Barca ya samu rauni a gwiwarshi bayanda yaci kwallo a wasansu da Birmingham.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce van Persie zai shafe makwanni uku yana jinya.

Yace"abin takaici, an dauki hoton kafarshi an gano zai yi jinyar makwanni uku".

Wannan raunin ba zai yiwa Arsenal dadi ba, gannin cewar tana shirin fuskantar Manchester United bayan ta kara da Barca.