2015:Zimbabwe ta janye daga neman daukar bakunci

mugabe Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe

Kasar Zimbabwe ta janye daga shiga takarar neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na mata a shekara ta 2015.

A watan daya gabata ne dai Zimbabwe ta sanarda cewa tana da aniyar daukar bakuncin sauran kasashen duniya.

Amma dai bisa dukkan alamu wannan matakin da Zimbabwe ta dauka bai rasa na saba rashin wajajen da za a dauki nauyin gasar.

Wannan matakin da kasar ta dauka na nufin cewar Canada ce kadai a halin yanzu ke neman a bata damar daukar bakuncin gasar.

A mako mai zuwa ne Fifa zata yanke hukunci akan kasashen da zasu dauki bakuncin gasanninta daban daban har guda biyar.