Alkalin wasan bai yi mana adalci ba - In ji Ferguson

Image caption Alex Ferguson

Kocin Manchester United Alex Ferguson ya ce hankalinsa bai kwanta ba a lokacinda aka zabi Martin Atkinson ya zama alkalin wasan da kungiyar za ta kara da Chelsea.

Chelsea dai ta doke Manchester United ne da ci biyu da daya a wasan da aka buga a filin Stamford Bridge.

Chelsea ta zura kwallo dayan da ya bata nasara ne a bugun Fennareti ana minti 80 da fara wasan.

"Muna bukatar alkalin wasan da zai yi adalci, kuma bamu samu hakan ba," In ji Ferguson.

"Da na ji an ce shi ne zai hura mana a wasan gaskiya hankalina bai kwanta ba."

Ferguson har wa yau ya ce ya fusata yadda alkalin wasan bai sallami dan wasan Chelsea, David Luiz ba, bayan da ya tadiye Rooney.

An dai sallami dan wasan United Vidic bayan an nuna masa katin gargadi na biyu a lokacin da ya tadiye Ramires.