Manchester United ta nuna sha'awar Neuer daga Schalke 04

neuer
Image caption Golan Jamus Manuel Neuer

Manchester United ta nuna sha'awar sayen golan Jamus Manuel Neuer daga kungiyar Schalke 04.

Schalke 04 ta ce "wani babban wakili ya bayyana cewar Manchester United nada muradi akan Neuer, kuma da zarar mun samu haka a rubuce zamu yi aiki akai".

Ba dai wannan ne karon farko da ake kallon Neuer a matsayin wanda zai maye gurbi Edwin van der Sar a Old Trafford.

A wannan watan ne Neuer zai cika shekaru 25, kuma kwangilarshi za ta kare ne a Schalke 04 a watan Yunin 2012, kuma akwai rahotannin dake nuna cewar Bayern Munich itama tana zawarcinshi.

Masana harkar kwallon kafa sun yi itifakin cewa kwarewar Neuer na daga cikin abinda ya baiwa Jamus nasara a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu inda ta samu kyautar tagulla.